ABUBUWAN MASU BAN MAMAKI A KAUNU (UNIVERSE):

 

Ƙaunu (universe) ta ƙunshi abubuwa masu ban-mamaki da dama, amma daga cikinsu akwai wasu da suke da wasu abubuwamasu matuƙar ban-al’ajabi.


1. GUGUWAR SHEKARU 186:


A duniyar Jupiter an taɓa yin wata fitinanniyar guguwa mai ban-tsoro, wacce kuma ba a taɓa gani ko jin labarin irin ta ba. Masana suka ce guguwar ta shafe shekaru 186 tana wakana a wannan duniyar, inda wani masani mai suna Giovanni Cassini ya fara gano hakan a shekakar 1665. Amma wasu masanan sun ce guguwar ta wakana ne a shekaru 356, wato daga shekarar 1665 zuwa 1713.


2. DUTSEN ZINARE:


Asteroid wani dutse ne da ke shawagi a sararin samaniya, musamman a matattararsa da ake ƙira Asteroid Belt. Haka nan yana yawo a duk wani wuri da zai iya zuwa a sararin samaniya. Abu mafi ban-mamaki shine akwai irin wannan dutsen wanda ya kasance na zinare ne zalla. Masana suka ce wannan Asteroid wanda ya kasance dutsen zinare mai suna PSYCHE 16 zai iya azurta kowa a duniyarmu (Earth).


3. DUNIYAR LU'ULU'U:


Wata duniya da ke ƙaunu (universe) da ta kasance ta lu’u-lu’u zalla tana ƙara ba wa mutane mamaki kullum. A Solar System wasu duniyoyi sun samu daga sinadaran hydrogen, da helium, da gas da makamantansu, amma ita wannan duniya mai suna 55-CANCRI babu abunda ta ƙunsa sai lu’u-lu’u zalla. Shin yaya duniyar za ta kasance saboda girman wannan arziƙin?


4. DUNIYAR RAYUWA (Earth):


A kaf faɗin ƙaunu babu wata duniya da ake rayuwa a cikinta face duniyar Earth. Ita ce duniyar da aka tabbatar da halittu suna rayuwa a cikinta. Ita ce duniyar da kominta yake daidai; zafi ko sanyi. Haka nan ita ce duniyar da ake ruwan sama.


Haƙiƙa wannan tsarin yana ba wa mutane mamaki musamman idan suka ji cewa ai duniyar Earth ce kaɗai inda ake rayuwa a halin yanzu, duk da masana suna ƙoƙarin gano wasu wurare da za a iya rayuwa bayan wannan duniyar, kamar binciken da masana ke yi a duniyar Mars.


ALLAH ALMUSAWWIRU KENAN!


NOTE: PICTURE (Mercury, the planet closest to sun).

Comments

Popular posts from this blog

Menene CAC Certificate?

Daga Bello Ado Hussaini

SOFTWARE