Posts

Showing posts from December, 2023

SOFTWARE

 SOFTWARE: Coding, Scripting and Programming, are they the same or not ? Dayawa mutane najin ana fadin CODING, SCRIPTING da kuma PROGRAMMING batareda sanin hakikanin me suke nufi ba, cikin wannan post zanyi bayanin akan me suke nufi sannan shin suna daukar ma'ana daya ne ko daban? CODING na nufin translating na wani yare zuwa wani yare, kamar misali Larabci zuwa Turanci, Hausa zuwa Larabci, shi ake kira da CODING, so duk lokacin da kayi building na application ko website, ana iya cewa kayi CODING na Application ko Website saboda kayi translating wani yare na computer zuwa wani yare. SCRIPTING shikuma ana amfani dashine domin ayi creating single or limited range of tasks,  usually ana amfani da SCRIPT ne domin ayi automation na wani task a computer, musamman automation, kamar misalin akyi creating SCRIPT wanda after every 30 minutes computer dinka tayi restarting na kanta, ko ta maka backup na wani abu, akwai programming languages da dama wadanda ake amfani dasu domin scripting...

ABUBUWAN MASU BAN MAMAKI A KAUNU (UNIVERSE):

  Ƙaunu (universe) ta ƙunshi abubuwa masu ban-mamaki da dama, amma daga cikinsu akwai wasu da suke da wasu abubuwamasu matuƙar ban-al’ajabi. 1. GUGUWAR SHEKARU 186: A duniyar Jupiter an taɓa yin wata fitinanniyar guguwa mai ban-tsoro, wacce kuma ba a taɓa gani ko jin labarin irin ta ba. Masana suka ce guguwar ta shafe shekaru 186 tana wakana a wannan duniyar, inda wani masani mai suna Giovanni Cassini ya fara gano hakan a shekakar 1665. Amma wasu masanan sun ce guguwar ta wakana ne a shekaru 356, wato daga shekarar 1665 zuwa 1713. 2. DUTSEN ZINARE: Asteroid wani dutse ne da ke shawagi a sararin samaniya, musamman a matattararsa da ake ƙira Asteroid Belt. Haka nan yana yawo a duk wani wuri da zai iya zuwa a sararin samaniya. Abu mafi ban-mamaki shine akwai irin wannan dutsen wanda ya kasance na zinare ne zalla. Masana suka ce wannan Asteroid wanda ya kasance dutsen zinare mai suna PSYCHE 16 zai iya azurta kowa a duniyarmu (Earth). 3. DUNIYAR LU'ULU'U: Wata duniya da ke ƙaunu (un...

Daga Bello Ado Hussaini

  MAQALA KO TAKARDAR DANA GABATAR A WAJEN TARON DOGARO DA KAI NA 25TH NOVEMBER, 2023. Aminu Kano Centre for Democratic Studies, CDC, Mambayya House, Kano. SANA'OIN GARGAJIYA DA TASIRIN SU WAJEN GINA ARZIKI MAI DOREWA A duk lokacin da aka ambaci Sana'oin gargajiya, abunda yake zuwa zuciyar mutane shine sana'oi na dauri wadanda muka gada iyaye da kakanni tun kafin zuwan turawa Nigeria ta Arewa,  Kamar; Saka Jima  Sassaka Rini Dukanci Ginin Tukunya Yar me ganye Wanzanci Aikin Kaba  Da sauransu. Amma yanzu Sana'oin gargajiya sun hada da wadancen ayyuka dana zayyana, da duk wata sana'a wadda ta shafi rayuwar Dan Adam ta yau da kullum, Kuma wadda dole ana bukatar ta a duk inda alumma ta hadu. Misali; Wadanda na fada a sama, sai Kuma; Aikin katako (Carpenter) Madinki (Tailor) Aikin famfo (plumber) Magini  (Builder) Aikin wuta  (Electrician) Kitso da gyaran Gashi (Saloon) Aski  (Barber shop) Sana'ar Abinci (Restaurant) Sai Kuma Shaguna na siyar da kayayyaki ka...

Menene CAC Certificate?

  CAC (Corporate Affairs Commission) shine Certificate ko kuma Shaidace da akeyiwa sana’a babba ko kuma ƙarama, wannan shaida ta CAC ita ke bada dama mai yawa a Gwamnatance ko daga bangaren kungiyoyi masu zaman kansu. Kowanne kasuwanci Yana kara inganta ne idan yakasance ya mallaki wannan shaidar ta CAC, kuma kowa kanyi kokarin hulda dakai batare da kokwanto, ko kuma tunanin cutarwa ba. A lokuta dayawa da suka wuce Gwanatin Tarayya da ta Jiha sukan ƙirƙiro wani tsare-tsare da za’a tallafawa ‘Yan kasuwa amma saboda rashin wannan shaida ta CAC kadan ne daga cikin Al’umma suke amfana, a bayannan Gwamnatin Tarayya ta fitar da tsarin Survival Fund amma wadanda suka mori tsarin cikin kwanciyar hankali sune wadanda suke da CAC Certificate.  A wannan gaba Nake  shawartar ƴan kasuwa manya da Kanana dasuje suyi wannan Certificate na CAC domin yana da matukar mahimmanci ga kasuwancin gida da waje. ✍️Yasir Mohammed Nasir