Daga Bello Ado Hussaini
MAQALA KO TAKARDAR DANA GABATAR A WAJEN TARON DOGARO DA KAI NA 25TH NOVEMBER, 2023.
Aminu Kano Centre for Democratic Studies, CDC, Mambayya House, Kano.
SANA'OIN GARGAJIYA DA TASIRIN SU WAJEN GINA ARZIKI MAI DOREWA
A duk lokacin da aka ambaci Sana'oin gargajiya, abunda yake zuwa zuciyar mutane shine sana'oi na dauri wadanda muka gada iyaye da kakanni tun kafin zuwan turawa Nigeria ta Arewa,
Kamar;
Saka
Jima
Sassaka
Rini
Dukanci
Ginin Tukunya
Yar me ganye
Wanzanci
Aikin Kaba
Da sauransu.
Amma yanzu Sana'oin gargajiya sun hada da wadancen ayyuka dana zayyana, da duk wata sana'a wadda ta shafi rayuwar Dan Adam ta yau da kullum, Kuma wadda dole ana bukatar ta a duk inda alumma ta hadu.
Misali;
Wadanda na fada a sama, sai Kuma;
Aikin katako (Carpenter)
Madinki (Tailor)
Aikin famfo (plumber)
Magini (Builder)
Aikin wuta (Electrician)
Kitso da gyaran Gashi (Saloon)
Aski (Barber shop)
Sana'ar Abinci (Restaurant)
Sai Kuma Shaguna na siyar da kayayyaki kamar;
Shagon Hatsi
Shagon masarufi (provisions)
Wajen Saida kayan Miya
Da sauransu.
Tasirin Wadannan sana'oi Dana lissafta a fagen tattalin arziki bazai misaltu ba, saboda kididdiga ta nuna sune suke daukar nauyin alumma ta wajen samun kudin shiga, sama da manyan kamfanoni da hukumomi, dama manyan sana'oi masu jari Mai kauri.
Kididdigar hukumar kula da Kanana da matsakaitan Sana'oi ta kasa Wato SMEDAN ta nuna cewa kaso 48% cikin 100 na karfin tattalin arzikin Nigeria Wato GDP yana fitowa ne daga Kanana da matsakaitan Sana'oi.
Ma'ana Kanana da matsakaitan Sana'oi na Samar da kusan Dollar Amurka biliyon 200, ko $201.6 billion a shekara.
Idan ka duba kusan da yawan mutane idan gari ya waye, kodai suna tafiya kasuwanni ne ko Kuma wajen da ake irin wadancen sana'oi da muka zayyana a shaguna kasuwanni da sauran gurare.
Lokaci bazai Bada dama mu dauki kowacce sana'a daya bayan daya, muce ga yadda za'a Zamanantar da ita ba, Wanda shine taken taron DOGARO DA KAI na wannan shekarar;
"ZAMANANTAR DA SANA'OIN GARGAJIYA,,
Amma dukkanin sana'oi ko kasuwanci suna da wata kama ta bai daya
Wato kamar mutum da mutum ne, ta yiwu su banbanta a launi ko tsayi ko suna, amma dukkanin su suna da bukata iri daya.
Suna bukatar abinci da sutura da wajen kwana da magani da mutunci da kwanciyar hankali.
To haka ma sana'oi suke da irin makamantan bukatu.
Don haka ga Wanda yake son ya inganta sana'ar sa yadda zata kula dashi, ta biya masa bukata, dole yabi wadannan matakan.
Na farko;
Matakin farko na sabunta sana'a da bunkasa ta shine NEMAN SHUHURA, ma'ana ka nemi shahara a cikin sana'arka, Wato suna.
Idan ka nemi suna cikin sana'arka to duk abunda kake so cikin sanaar zaka samu.
Saboda shuhura ita take kawo abokan hulda, abokan hulda su ke kawo ciniki, ciniki Kuma shike kawo riba, riba Kuma ita ke tara arziki da bunkusa ayyukan sana'a
MISALI;
Na Gujungu Mai shayi a sashin gidan zoo dake Kano.
Na Gujungu ya kirkiro wasu dabaru da hikimomi wadanda suka sa yayi shuhura a cikin sana'ar shayi da burodi a duk fadin Birnin Kano da kewaye, cikin dubban masu wannan sana'a Kuma tabbas ta tara masa arziki mai yawa
Mataki na biyu;
YA AKE NEMAN SHUHURA?
Sai ka banbanta ayyukan ka dana saura cikin tsari da inganci da sakamako Wato results
Ya zamana yadda kake tafiyar da al'amuran ka na kasuwanci sun Saba daga yadda aka Saba ganin su.
Mataki na uku;
YA ZAKA SABUNTA AYYUKAN KA SU ZAMA DABAN DANA SAURA?
Dole ka zama Mai abu biyu.
KIRKIRA DA BIBIYA.
(Innovation n Creativity.)
Ka zama kullum cikin kirkiro wasu hanyoyi da ayyukan ka zasu Kara aminci da kyau, ka zama Mai bibiyar duk inda ake yin irin sana'ar ka a fadin duniya, ta hanyar karance karance da bibiyar (following) shafukan masu irin sana'ar taka a shafukan sada zumunta, (Social media) da Kuma sauraren kwararru.
MISALI;
JEEVES OF BELGRAVIA
LONDON FINEST DRYCLEANERS
Na bayar da labarin wannan gidan wanki da guga dana ziyarta a birnin London dake England a shekarar 2019.
Wannan gidan wanki da guga ya shafe shekara sama da 50 yana aiki, Kuma kamar yadda nayi bayani tsarin wajen yafi duk Wani zauren banki daka taba gani Wato (Banking Hall) tsari da Kaye musamman anan jihohin mu na Arewa.
Zaku iya duba wannan kamfani ta yanar gizo Wato Google don ganin hotuna da ayyukan su.
MATAKI NA 4
WARE KASO CIKIN RIBA DAN SAYEN KAYAN AIKI..
(RETAIN EARNINGS)
Wato ya zama kana ware Wani kaso na ribar da kake samu wajen Samar da kayan aiki da kuma bunkasa muhallin da kake yin sana'ar ka a wajen.
Wannan yana da muhimmanci kwarai wajen cigaba da Samar da sakamako na bai daya a kullum ga abokan huldar ka.
shine (CONSISTENCY DA CONTINUITY)
NA 5
Bayan duk ka cimma wadancen matakai guda 4, akwai abu guda daya Wanda zai iya hana wadancen hudun tasiri ko yasa suyi aiki.
Shine;
KYAUTATA MU'AMALA DA TSARE GASKIYA. DA CIKA ALKAWARI
MISALI;
Akwai daya daga cikin kamfanin hada abincin dabbobi da kaji mafi girma da shahara a Nigeria, Wanda kamfanin mu yake samarwa da sinadarai na ayyukan su, akan tsari na supply.
Tsarin supply shine kamfani ta baka order Wato LPO bayan ka Kai kaya Kuma an gamsu da ingancin abunda ka kawo sai a biya ka.
Amma wannan shahararren kamfani saboda gamsuwa da yanayin kayan da muke basu, akwai lokacin da suka bawa kamfanin mu tsabar kudi don mu tattara musu kaya ba tare da haufin ingancin abunda zamu kawo ba.
Hakan ya biyo bayan yarda da gamsuwa da suka samu a ayyukan mu na tsahon lokaci.
NB; Na sakaya sunan kamfanin saboda ka'idar rufe sirrin abokin ciniki.
RUFEWA (CONCLUSION)
Mai sana'a yana bukatar ya siffantu da wasu dabi'u da zasu taimake shi, kaiwa ga nasara ko Kuma dabbaka wadancen matakai da aka zayyana.
Shine ka zama kana da (passion) Wato sha'awa Mai karfi akan sana'ar da kake yi.
Sunce;
"Entrepreneurship is a lifestyle.,
Ka zama cewa ka gamsu duk abunda kake son ka zama a rayuwa kana tunanin wannan sana'ar zata yi Maka shi.
Ina yawan fadi cewa, kowacce sana'a akwai Dangote a cikin ta.
Ka zama mai alfahari da sana'ar da kake yi a ko Ina.
MISALI;
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Kuma tsohon sanata Engr Rabiu Musa Kwankwaso, yana yawan fadin cewa shi injiniyan ruwa ne.
Wani lokaci ya taba cewa cikin jama'a duk Kano da wuya a Sami Plumber kwararre kamar sa.
Yace kunga idan na cire riga, na kama aikin famfo, zaku Sha mamaki, duk da matsayin da Allah yayi masa a rayuwa.
Nagode
DOGARO DA KAI
25th November, 2023
Kano Nigeria
Comments
Post a Comment