Menene CAC Certificate?

 

CAC (Corporate Affairs Commission) shine Certificate ko kuma Shaidace da akeyiwa sana’a babba ko kuma ƙarama, wannan shaida ta CAC ita ke bada dama mai yawa a Gwamnatance ko daga bangaren kungiyoyi masu zaman kansu.


Kowanne kasuwanci Yana kara inganta ne idan yakasance ya mallaki wannan shaidar ta CAC, kuma kowa kanyi kokarin hulda dakai batare da kokwanto, ko kuma tunanin cutarwa ba.


A lokuta dayawa da suka wuce Gwanatin Tarayya da ta Jiha sukan ƙirƙiro wani tsare-tsare da za’a tallafawa ‘Yan kasuwa amma saboda rashin wannan shaida ta CAC kadan ne daga cikin Al’umma suke amfana, a bayannan Gwamnatin Tarayya ta fitar da tsarin Survival Fund amma wadanda suka mori tsarin cikin kwanciyar hankali sune wadanda suke da CAC Certificate. 


A wannan gaba Nake  shawartar ƴan kasuwa manya da Kanana dasuje suyi wannan Certificate na CAC domin yana da matukar mahimmanci ga kasuwancin gida da waje.


✍️Yasir Mohammed Nasir

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Daga Bello Ado Hussaini

SOFTWARE